Akalla mutum 24 ne suka rasa rayukansu yayin wani mummunan hari da aka kai a ƙauyen Debe da ke ƙaramar hukumar Shanga a jihar Kebbi.
Jaridar Punch ta rawaito cewa a cikin wata sanarwa da aka fitar a Yauri, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar 5 ga watan Afrilu, inda wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai farmaki, suka yi ajalin mutane tare da lalata dukiyoyi da dama.
Rahotanni sun nuna cewa wannan hari shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren da ke faruwa a yankunan kan iyaka tsakanin jihohin da Neja.
