Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiYan kasuwar mai sun sauke farashin man fetur kasa da yadda Dagote...

Yan kasuwar mai sun sauke farashin man fetur kasa da yadda Dagote ke sayarwa

Wasu masu shigo da man fetur daga ƙasashen waje sun fara sayar da shi a ƙasa da Naira 860 kowace lita, lamarin da ya sauka daga farashin masana’antar Dangote da ke tsakanin N865 zuwa N875 a Legas da Ogun.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kamfanonin Aiteo da Menj sun sayar da man a N815, yayin da Dangote ke sayarwa a N820. Wannan sauyin farashi na nuna ci gaba da ƙara gasa a kasuwar mai ta Najeriya.

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Alhaji Aliko Dangote ke kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da shigo da fetur daga ketare, domin kare masana’antarsa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata