‘Yan Majalisar Wakilai 6 daga Jihar Rivers sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda suka danganta matakin da rikicin shugabanci da rabuwar kai da ke addabar PDP.
Wadanda suka sauya sheka sun hada da Dumnamene Dekor, Cyril Hart Godwin, Solomon Bob, Victor Obuzor, Blessing Amadi da Felix Uche, inda Kakakin Majalisar, Hon. Abbas Tajudeen, ya karanta wasiƙunsu a zaman majalisar ranar Talata.
‘Yan majalisar sun ce rikice-rikicen cikin gida a PDP sun hana su cimma muradunsu na siyasa da na majalisa. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu ‘yan majalisa 4 daga Rivers sun koma APC daga PDP da LP, lamarin da ya ƙara raunana jam’iyyun adawa a jihar.
Masu lura da siyasa na alakanta wannan sauya sheka da sabon jeri na siyasa a Rivers bayan Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya koma APC.
Da wannan sabon ci-gaba, ‘yan PDP uku kaɗai suka rage daga Rivers a Majalisar Wakilai, wato Shugaban ‘Yan Adawa Kingsley Chinda, Kelechi Nworgu da Anderson Allison Igbiks.
