Monday, April 6, 2026
HomeLabarai'Yan majalisar dokokin Nijeriya biyu sun bar Labour Party zuwa APC

‘Yan majalisar dokokin Nijeriya biyu sun bar Labour Party zuwa APC

Jam’iyyar Labour Party ta sake rasa wasu ‘yan majalisa guda biyu da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, a daidai lokacin da sauye-sauyen siyasa ke kara kamari gabanin babban zaben 2027.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio a ranar Alhamis ya sanar da sauya shekar Sanata Neda Imasuen, mai wakiltar Edo ta Kudu, yayin zaman majalisar a Abuja.

A cikin wasikar da ya aike wa majalisar dattawa, Imasuen ya ce matakin nasa ya biyo bayan tattaunawa da al’ummarsa da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da kuma magoya bayansa.

Shima dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa/Kudu Chimaobi Atu, ya fice daga jam’iyyar Labour zuwa APC.

Kakakin majalisar Tajudeen Abbas ne ya sanar da sauya shekar sa a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Atu, ya alakanta ficewarsa da rikicin cikin gida na jam’iyyar Labour, wanda ya ce ya yi illa ga ayyukansa na majalisa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata