Monday, April 6, 2026
HomeLabarai’Yan Majalisar Rivers sun ƙuduri aniyar ci gaba da tsige Fubara

’Yan Majalisar Rivers sun ƙuduri aniyar ci gaba da tsige Fubara

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Rivers sun jaddada ƙudurinsu na ci gaba da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara, bayan wasu ’yan majalisa huɗu da suka ja da baya tun farko sun sake mara wa shirin baya.

’Yan majalisar huɗun — Sylvanus Nwankwo (Omuma), Peter Abbey (Degema), Barile Nwakoh (Khana I) da Emilia Amadi (Obio/Akpor II) — sun bayyana a tsakanin Litinin da Laraba cewa sun fice daga shirin tsige gwamnan ne domin tattaunawa da sulhu.

Sai dai a zaman majalisa da aka gudanar ranar Juma’a, ’yan majalisar huɗun sun janye matsayinsu na baya, suna zargin gwamnan da mataimakinsa da ci gaba da nuna adawa, tare da yin watsi da kiran da ake yi na shiga tattaunawa.

Bayan haka, majalisar ta kaɗa ƙuri’a baki ɗaya inda ta amince da ci gaba da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara, lamarin da ke ƙara tsananta rikicin siyasar da ke addabar jihar Rivers.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata