Monday, April 6, 2026
HomeSiyasa'Yan majalisar wakilai 8 na LP da PDP sun sauya sheka a...

‘Yan majalisar wakilai 8 na LP da PDP sun sauya sheka a jihohin Delta da Enugu

A ranar Talata ‘yan majalisar wakilai takwas suka bayyana ficewa daga jam’iyyunsu zuwa wasu jam’iyyu daban-daban.

‘Yan majalisar wakilai 6 daga jihar Delta sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, yayin da ‘yan majalisa biyu daga jihar Enugu suka bar jam’iyyar Labour suka koma PDP.

A yayin zaman majalisar na yau talata ne aka karanta sanarwar ficewar ‘yan majalisar.

Wadanda suka sauya sheka daga jihar Delta sun hada da Nicholas Mutu Bomadi da Nnamdi Ezechi, Jonathan Okodiko, Thomas Eriyetomi, Julius Pondi, da kuma Victor Nwokolo.

‘Yan jam’iyyar Labour da suka koma PDP sun hada da Mark Obetta daga Enugu da Dennis Agbo.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata