Sunday, April 5, 2026
HomeLabarai'Yan majalisar wakilai sun nemi gwamnatin tarayya ta gina sansanin sojoji a...

‘Yan majalisar wakilai sun nemi gwamnatin tarayya ta gina sansanin sojoji a Yelwata da ke jihar Benue

Majalisar Wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kafa sansanin sojojin Nijeriya a garin Yelwata dake kan iyaka a karamar hukumar Guma ta jihar Benue, biyo bayan halaka mutane da ake zargin wasu mahara dauke da makamai suka yi wa sama da mutane 200 a ranar 14 ga watan Yuni.

Wannan kudiri dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Makurdi/Guma,a majalissar Dickson Tarkighir ya gabatar.

Dan majalisar ya kuma yi tir da mummunan harin, yana mai nuni da cewa kisan kiyashin na Yelwata ya kara dagula harkokin jinkai a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata