Monday, April 6, 2026
HomeSiyasa’Yan majalisar wakilan Nijeriya 3 na PDP sun sauya sheka zuwa APC

’Yan majalisar wakilan Nijeriya 3 na PDP sun sauya sheka zuwa APC

Wasu ‘yan majalisar wakilai uku daga jam’iyyar PDP sun koma APC a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Laraba, suna zargin rikicin cikin gida da rashin shugabanci a jam’iyyar PDP.

Wadanda suka sauya sheka su ne: Sanata Taofeek Ajilesoro, da Sanata Emmanuel Olusanya daga Jihar Osun sai Sanata Marcus Onobun daga jihar Osun Jihar Edo.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ambato mambobin na cewa sun dauki matakin ne domin hada kai da Shugaba Tinubu wajen cika alkawuran dimokuradiyya ga mazabunsu.

Wannan na zuwa a lokacin da PDP ke fuskantar matsin lamba, yayin da APC ke kara samun rinjaye a majalisar wakilai da ta dattawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata