DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeLabarai'Yan Najeriya 7,646 sun nemi mafaka a Sweden cikin shekaru 24

‘Yan Najeriya 7,646 sun nemi mafaka a Sweden cikin shekaru 24

Hukumar kula da shige da fice ta Sweden ta ce ‘yan Najeriya sama da 7,646 ne suka nemi mafaka a kasar cikin shekaru 24.

Wasu bayanai da jaridar Punch ta tattaro daga shafin yanar gizo na hukumar, sun nuna cewa a tsawon wannan lokaci, ‘yan Najeriya na ci gaba da tururuwar neman mafaka a kasar.

Kazalika bayanan sun nuna cewa a nahiyar Afirka, Najeriya na cikin jerin kasashe 5 da al’ummarta suka fi yawan neman mafaka a kasar.

Sudan, Somalia, Eritrea da kuma Ethiopia su ne kan gaba sakamakon ta’azzarar matsalolin tsaro da na tattalin arziki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata