Monday, April 6, 2026
HomeSiyasa’Yan Najeriya sun yi kuskure a kayar da gwamnatin Jonathan - Dr....

’Yan Najeriya sun yi kuskure a kayar da gwamnatin Jonathan – Dr. Grema Kyari

Ƙungiyar Bring Back Our Goodluck ta bukaci tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, da ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaben 2027.

Da yake jawabi a taron manema labarai a Mambayya House da ke Kano, shugaban ƙungiyar, Dr. Grema Kyari, ya ce ’yan Najeriya sun yi kuskure a 2015 wajen kawar da gwamnatin Jonathan ta hanyar ƙuri’a.

Ƙungiyar ta bayyana cewa mulkin Jonathan ya fi samar da kwanciyar hankali da bunƙasar tattalin arziki, inda aka samu farashin kayan abinci da mai a farashi mai sauƙi, tare da shirye-shiryen tallafawa matasa kamar YouWin! da SURE-P.

Kyari ya ce dawowar Jonathan ya zama dole, yana kwatanta shi da dawowar Donald Trump a Amurka da John Mahama a Ghana.

Ya kuma ƙara da cewa, a lokacin Jonathan, buhun shinkafa na sayarwa kusan N7,800, amma a yau ya kai tsakanin N80,000 zuwa N100,000, lamarin da ya jefa miliyoyin ’yan ƙasa cikin yunwa da talauci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata