Sunday, April 5, 2026
HomeLabarai'Yan Nijeriya miliyan 19.2 su ka rungumi shirin inshorar lafiya

‘Yan Nijeriya miliyan 19.2 su ka rungumi shirin inshorar lafiya

Hukumar kula da shirin inshorar lafiya ta Nijeriya ta ce ‘yan kasar 19.2 ne su ka yi rajista a karkashin shirin, adadin da ya zarce wanda ta yi hasashen samu a cikin shekara ta2014.
Darakta Janar na hukumar NHIA, Dr Kelechi Ohiri ne ya bayyana hakan a Abuja, lokacin wani taron ranar kula da lafiyar al’umma ta duniya domin bita akan irin ci gaban da ake samu a bangaren kiwon lafiya.
A cewarsa, da wannan nasarar da Nijeriya ta samu na waɗanda suka shiga tsarin inshorar lafiya, ta cimma kashi 95 na hasashen da take son samu a shekarar 2027.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata