Tuesday, April 7, 2026
HomeLabarai'Yan Nijeriya na bukatar sabbin jini, ba tsofaffin 'yan siyasa ba - Laolu Akande

‘Yan Nijeriya na bukatar sabbin jini, ba tsofaffin ‘yan siyasa ba – Laolu Akande

Yayin da hankulan siyasa ke kara karkata zuwa zabukan 2027, tsohon mai taimakawa shugaban kasa, Laolu Akande, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su gujewa zaben tsofaffin ‘yan siyasa, yana mai cewa lokaci ya yi da za a bai wa sabbin fuskoki dama domin kawo kyakkyawan tsari na gyare-gyare da manufofi masu ma’ana.

Da yake magana a shirin Sunrise Daily na Channels Television a ranar Alhamis, Akande ya nuna damuwa kan halin da bangaren adawa ke cikin a kasar.

Ya bayyana cewa jam’iyyun adawa na ci gaba da amfani da tsofaffin dabarun siyasa wadanda ba sa kara wa al’umma kwarin gwiwa ko samar da hanyoyin da suka bambanta da na yanzu.

Akande ya bukaci matasa da masu kishin kasa da su fara shirye-shiryen samar da sabbin shugabanni masu nagarta da hangen nesa gabanin 2027.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata