DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan Nijeriya sun yi ”wawa” a wajen rabon kayan tallafi

-

Google search engine

Wasu mutane a jihar Bayelsa da ke Najeriya sun fasa tare da wawushe rumbun tara hatsi da sauran kayan abinci da gwamnatin jihar ta killace a birnin Yenagoa domin raba wa jama’a da zummar rage radadin ibtila’in ambaliyar ruwa tun a 2022. 

RFI Hausa wacce ta ruwaito wannan labarin ta ce gwamnatin jihar ta ce wasu daga cikin kayan abincin sun fara lalacewa. 

An fasa rumbun ne da ke kan babbar hanyar Isaak Boro a Yenagoa saboda irin tashin hankalin da al’umar ke ciki na hauhawar farashn kayayyakin masarufi wanda ya samo asali daga cire tallafin man fetur da ya haddasa tsananin tsadar rayuwa. 

Janye tallafin ne ya sa farashin man fetur  ya yi tashin goron-zabi daga N190 zuwa 620 kan kowacce lita wanda hakan ya shafi farashin motocin sufuri da kayan abinci da sauransu.

Sai dai Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Bayelsa ta bayyana cewa wadannan kayayyakin abincin da aka kwashe ba su da ingancin da za a iya aci, domin sun lalace don haka duk wanda ya ci zai fuskanci matsala. 

PUBLICITÉ

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatinmu na cika alkawura da zummar mayar da Najeriya jigo a harkar noma a Duniya – Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya za ta hada kai da abokan huldarta na kasa da kasa domin bai wa matasan kasar...

Kungiyar Sanatocin Arewa ta yi tir da kisan da aka yi wa wasu matafiya 12 da suka fito daga jihar Kaduna

Kungiyar Sanatocin Arewa ta yi Allah-wadai da ajalin matafiya 12 'yan jihar Kaduna da wasu suka yi a jihar Filato yayin da suke tafiya daurin...

Mafi Shahara