Wednesday, April 8, 2026
HomeLabarai'Yan Nijeriya sune na 5 wajen karamci a fadin duniya - Wani...

‘Yan Nijeriya sune na 5 wajen karamci a fadin duniya – Wani rahoto

A cewar sabon rahoton Global Giving Index 2024, Najeriya ta dare matsayi na biyar a jerin ƙasashe mafi ƙaramci, inda ga shige gaba ƙasashe irin su Amurka da Ostiraliya.

Wannan wata alama ce da ke bayyana yadda al’ummar Najeriya ke rayuwa da juna cikin tausayi, taimako da sadaukarwa.

Taimakon da ƴan Najeriya ke yi da kafa kungiyoyin sa kai a kafar sada zumunta haɗi da masallaci, coci, ko a kasuwa ba, sun zama al’ada, duk kuwa da matsin rayuwa, da rashin wadata da ake fama da su, a cewar rahoton.

Ƙasashen Kenya da Gambia su ne kaɗai suka fi Najeriya a yankin Afrika.

Rahoton ya fito ne daga kungiyar Charities Aid Foundation (CAF) wanda ya binciko halayen karamci, taimako ga baƙi da aikin sa kai a faɗin duniya.

Jerin ƙasashe 10 mafi karamci a fadin duniya sun hada da:

1. Indonesia
2. Kenya
3. Singapore
4. Gambia
5. Nigeria
6. Amurka
7. Ukraine
8. Australia
9. Hadaddiyar Daular Larabawa
10. Malta

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata