Monday, April 6, 2026
HomeLabarai‘Yan sa kai a jihar Zamfara sun yi ajalin kasurgumin dan bindiga...

‘Yan sa kai a jihar Zamfara sun yi ajalin kasurgumin dan bindiga Kachalla Yellow Danbokolo

Sanannen shugaban ‘yan bindiga, Kachalla Yellow Danbokolo, ya rasa ransa a Zamfara bayan harbin da ya sha a artabu da dakarun sa-kai na Shinkafi.

Danbokolo, wanda ake ganin ya fi Bello Turji hatsari, rahoton jaridar the Nation yace dan kawun Bello Turjin ne, wanda aka yi ajalinsa a karshen mako, tare da ‘yan bindiga 173 da suka rasu a samamen.

Labarin kawar da Danbokolo ya haifar da murna a Kurya da sauran yankunan da ya addaba, inda jama’a ke cewa shi ne jagoran manyan hare-hare, yayin da Turji ya yi kaurin suna wajen yada farfaganda a harin da yake kaiwa kayukan yankin na Arewa maso yamma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata