Monday, April 6, 2026
HomeLabarai'Yan sanda a Dubai sun kama wadanda ake zargi da satar wani...

‘Yan sanda a Dubai sun kama wadanda ake zargi da satar wani Lu’u-lu’u da darajarsa ta kai Dalar Amurka miliyan 25 A ranar Litinin ne ‘yan sanda

 

A ranar Litinin ne ‘yan sanda suka yi nasarar chafke wasu barayi uku awa daya bayan sun sace wata sarkar Lu’u-lu’u da darajar kudin ta ya kai Dalar Amuruka Miliyan 25

A cikin wata sanarwa ta ofishin dillancin labarai na WAM a hadaddiyar Daular Larabawa, rundunar yan sandan ta bayyana cewa ta kama barayin biyo bayan sace Lu’u-lu’un wanda wani dan kasuwar lu’u-lu’u ya kawo daga turai.

Rahoton ya nuna cewa barayin sun janyo dan kasuwar zuwa wani gida a Dubai, da sunan nuna lu’u-lu’un ga wani abokin ciniki mai dukiya, wanda hakan ya basu damar satar.

Yan sanda sun ce sun gudanar da binciken gaggawa biyo bayan lamarin, wanda ya kai ga nasarar cafke mutanen uku da ake zargi da hannu a lamarin, tare da kwato lu’u-lu’un ba tare da wata matsala ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata