Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama mutum uku tare da kwace wasu kayayyakin fashewa a wani samame da ta gudanar bisa umarnin IGP Kayode Egbetokun na ƙara sintiri da aikin leken asiri a manyan hanyoyi.
An kama motar kirar Golf dauke da detonators 6,975 a Koza, karamar hukumar Daura, wadda Jamilu Musa Mai shekaru 40 ke tukawa.
Bincike ya gano cewa ya ɗauko kayan ne daga Kano zuwa Kwangolam, da ke karamar hukumar Mai’adua ta jihar.
Sanarwar ta ce bayan zurfafa bincike, rundunar ta cafke wasu karin mutum biyu Ibrahim Murtala dan shekaru 22 da Sulaiman Muhammad mai shekaru 35, inda aka ƙara kwato detonators 7,500 da jakunkunan gelatine 30½ masu nauyin 2,273.65 kg.
Dukkansu sun amsa laifinsu, kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda suka tsere, in ji jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu.
