Hadakar ‘yan sanda, jami’an tsaron sirri na DSS, sojoji da jami’an C-Watch hade da ‘yan banga a jihar Katsina sun yi nasarar kubutar da mutane 11 da aka sato don garkuwa da su.
Lamarin ya faru ne a lokacin da jami’an ke sintiri kan titin Danmusa zuwa Mara zuwa Dangeza a cikin karamar hukumar Danmusa jihar Katsina.
