Monday, April 6, 2026
HomeLabarai’Yan sanda sun cafke wani dan kungiyar Lakurawa tare da kwato shanu...

’Yan sanda sun cafke wani dan kungiyar Lakurawa tare da kwato shanu a Kebbi

Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta samu nasarar cafke wani da ake kyautata zaton ɗan kungiyar Lakurawa ne, tare da kwato shanu 10 daga cikin 68 da aka sace a kauyen Zogirma dake karamar hukumar Bunza.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa an cafke wanda ake zargi mai suna Salihu Umar ɗan asalin Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, a kasuwar dabbobi ta Bachaka yayin da yake ƙoƙarin sayar da shanun da aka sace mallakar wani manomi mai suna Usman Aliyu na Zogirma.

Ya ce barayin sun sace shanun ne sannan suka tsallaka da su zuwa Jamhuriyar Nijar, kafin daga bisani wanda ake zargi ya dawo domin sayar da wani ɓangare daga cikinsu, inda jami’an tsaro suka kama shi bayan samun bayanan sirri.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata