Sunday, April 5, 2026
HomeLabarai'Yan sanda sun ce sun kama mutumin da ya cefanar da jaririnsa...

‘Yan sanda sun ce sun kama mutumin da ya cefanar da jaririnsa Naira milyan daya da rabi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi ta ce ta kama wani mutum mai matsakaitan shekaru mai suna Chukwuma Onwe bisa zargin sayar da ɗansa mai kwanaki biyar da haihuwa kan kudi Naira miliyan 1.5.

Bayanai sun ce, an cafke Onwe ɗan asalin garin Nwezenyi-Igbeagu da ke ƙaramar hukumar Izzi a jihar, ne bayan matar da yake shirin aura, Philomena Iroko, ta sanar da maƙwabcinta, wanda kuma ya kai rahoto ga ‘yan sanda game da abin da mijin ya aikata.

Rahotanni sun nuna cewa jaririn, an sayar da jaririn namijin ne ga wata mace mai suna Chinyere Ugochukwu, wadda ita ma ‘yan sanda suka kama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata