Monday, April 6, 2026
HomeKetare'Yan sanda sun damke wani dan Najeriya kan zargin damfarar mata sama...

‘Yan sanda sun damke wani dan Najeriya kan zargin damfarar mata sama da 100 a India

Jam’ian ‘yansandan India sun damke wani dan Najeriya da ake zargi da damfarar mata sama da 100 a kasar.

Jaridar Hindustan Times ta ruwaito cewa, ana zargin matashin dan shekaru 29 mai suna Stephane da yaudarar matan a matsayin wani babban dan kasuwa da ke zaune a kasar Burtaniya.

Rahotanni sun ce dan Najeriyar kuma na amfani da sunan ‘Dominic’ da ‘Duck Young’ wajen dana wa matan tarko.

An yi zargin cewa ya tatsi manyan kudade daga matan da ya yaudara a kasar ta India kafin fadawa komar hukuma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata