Monday, April 6, 2026
HomeSiyasa‘Yan sanda sun hana taron murnar zagayowar ranar haihuwar Peter Obi a...

‘Yan sanda sun hana taron murnar zagayowar ranar haihuwar Peter Obi a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta hana wani taron da magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, suka shirya don murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana cewa rahoton sirri ya nuna wasu bata-gari na shirin kitsa taron domin tayar da tarzoma da tada hankalin jama’a.

Ya ce dukkannin taruka da ke da alaka da siyasa a jihar za su ci gaba da kasancewa a dakace har zuwa lokacin da hukumar zabe INEC ta bayyana a hukumance a fara yakin neman zabe.

Rundunar kamar yadda jaridar Channels ta ruwaito ta ce taron zai iya rikitar da wasu wuraren da jam’iyyun siyasa suka tanada domin gudanar da zaben fidda gwani da aka shirya a rana ɗaya da taron na Obi, wanda hakan na iya haifar da rikici da rashin tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata