Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekara 30 bisa zargin sayar da jaririn ‘yar uwarsa ɗan wata guda a kan kudi Naira miliyan biyu.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN, ya rawaito cewa wanda ake zargin, mazaunin Igbogbo, Ikorodu, ya bayyana cewa ya sayar da jaririn ne domin samun kudin da za a yi jana’izar mahaifiyarsu.
Lamarin ya fito fili ne bayan mahaifiyar jaririn ta kai korafi ga ‘yan sanda.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olohundare Jimoh, ya umarci a mika binciken shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar, wato SCID, da ke Panti, domin zurfafa bincike kan lamarin.
