Mutumin mai suna Lekan Lasisi ya shiga hannun ’yan sanda a jihar Ogun bayan da wata rigima tsakaninsa da ɗan’uwansa kan bashin Naira 4,000 ta yi sanadin mutuwar ɗan’uwan.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a Unguwar Abule Tuntun, cikin karamar hukumar Odeda ta jihar Ogun.
Bincike ya nuna cewa rikicin ya fara ne bayan da Lasisi ya fusata, sakamakon haka ɗan’uwan nasa ya fara fito da adduna, shi kuma wajen kare kansa ya fitar da bindiga, inda ya ce bindigar ya harba ta ne ba tare da niyya ba, harsashin kuma ya samu ɗan’uwansa wanda daga bisani ya rasu.
