Monday, April 6, 2026
HomeKetare‘Yan sandan Uganda sun ƙaryata kama jagoran adawa yayin da Museveni ke...

‘Yan sandan Uganda sun ƙaryata kama jagoran adawa yayin da Museveni ke tunkarar sake lashe zaɓe da rinjaye

Rundunar ‘yan sandan Uganda ta musanta ikirarin da jam’iyyar adawa ta NUP ta yi cewa an kama jagoranta, Bobi Wine, a daidai lokacin da Shugaba Yoweri Museveni ke gab da sake lashe zaɓen ƙasar da rinjaye.

Jam’iyyar National Unity Platform (NUP) ta Bobi Wine ta ce a daren Juma’a wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojoji ya sauka a harabar gidansa da ke Kampala, inda suka “tilasta shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.” Sai dai kamfanin dillancin labarai Reuters ya ce bai samu damar tabbatar da wannan ikirari nan take ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ƙasar, Kituuma Rusoke, ya bayyana a wani taron manema labarai da aka watsa kai tsaye cewa Bobi Wine yana gidansa kuma yana da ‘yancin motsi.

Har lokacin rubuta wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin Bobi Wine ko wakilan jam’iyyar NUP ba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata