Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasa‘Yan siyasa na bayyana kadarorin da ba su mallaka ba kafin hawa...

‘Yan siyasa na bayyana kadarorin da ba su mallaka ba kafin hawa Mulki – EFCC

Shugaban hukumar da ke yaki da yiwa tattalin arzikin kasa tu’annati EFCC, Ola Olukoyede, ya ce wasu ‘yan siyasa na amfani da dabara ta bayyana kadarorin da ba su mallaka ba kafin su hau mulki, domin su kauce wa binciken rashawa.

Wannan ya biyo bayan wani taro na kaddamar da kayan aiki na yanar gizo kan dokokin ma’aikatan gwamnati a Abuja, wanda Olukoyede ya bayyana cewa bincike ya gano wani babban jami’i ya saka adireshin gida daban a takardun bayyana kadarori, duk da cewa gidan bai wanzu ba a zahirance.

Rahoton jaridar Daily Trust ya tattaro yadda daga baya aka gano cewa bayan lashe zabe, jami’in ya gina kadarar a wani adreshi na daban, wanda ya dace da wanda yake nufi tun farko.

Wannan dabara, in ji shi, ana kiranta da “anticipatory declaration of assets” wato bayyana kadarorin da ake shirin mallaka nan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata