Monday, April 6, 2026
HomeWasanni’Yan wasan dambe biyu sun rasu sakamakon raunin kwakwalwa yayin wassanin Tokyo

’Yan wasan dambe biyu sun rasu sakamakon raunin kwakwalwa yayin wassanin Tokyo

’Yan damben Japan, Shigetoshi Kotari da Hiromasa Urakawa, duk masu shekaru 28, sun rasu bayan samun mummunan raunin kwakwalwa a fafatawa daban-daban da aka gudanar a Korakuen Hall, Tokyo, ranar 2 ga Agusta.

Rahoton Channels TV ya ce Kotari ya fadi bayan kammala zagaye na 12 da Yamato Hata, inda ya rasu a ranar 8 ga Agusta sakamakon acute subdural haematoma.

Urakawa kuwa, wanda aka dakatar a zagaye na takwas da Yoji Saito, ya rasu bayan kwana biyu.

Hukumomi sun ce wannan na iya zama karo na farko a Japan da ’yan dambe biyu a cikin gasa guda suka bukaci tiyata a kwakwalwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata