Kotun kolin kasar Kenya ta yanke hukunci cewa yara da aka haifa ba tare da aure ba daga mahaifi Musulmi suna da ‘yancin gado daga dukiyar mahaifinsu.
Wannan hukunci da kotun ta yanke ya daidaita tsarin dokar Musulunci da kundin tsarin mulkin kasar.
DW Afirka ta ruwaito cewa shari’ar ta samo asali ne daga wata mata da ke kokarin hana yaran mijinta da ya rasu da wasu mata biyu gado, tana mai cewa ba su da hurumi a dokar Musulunci.
Sai dai kotun ta yi watsi da karar, tana mai cewa hakan ya saba wa tsarin adalci da daidaito da kuma dokar hana wariya da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar.
