Wani binciken kwararru ya yi nuni da cewa yaran da ke cin abinci sai daya a rana na cikin hadarin kamuwa da raunin kwakwalwa.
Masanan sun kuma ce rashin samun abinci mai gina jiki na shafar yanayin yaran, musamman ta fuskar kwazo, dabi’u da dai sauran su.
Sun kara da yin kira ga iyaye su kokarta wajen samar wa da yaran su abinci mai gina jiki kuma a wadace, domin tabbatar cewa sun samu ingantacciyar lafiya.
