Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana titin Lagos-Calabar da gwamnatin Tinubu ke ginawa a matsayin “zamba”, yana zargin gwamnati da gaza aiwatar da ayyukan da ke amfani wa ‘yan kasa.
A wata hira da ya yi a shirin Inside Sources na Channels TV, Lawal ya ce babu wani babban aiki da gwamnatin ke yi wanda ke da tasiri a rayuwar jama’a, musamman a Arewa inda ya ce babu hanyoyin da ake ginawa ko gyarawa.
Ya kara da cewa, “Kowa ya san tun kafin fara aikin titin tekun, mutane sun fahimci cewa zamba ce. Kuma yanzu abin da ya fara fitowa fili, ya zama zamba.”
