Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaYawaita buga sabbin takardun kudi da da aka rika yi a gwamnatin...

Yawaita buga sabbin takardun kudi da da aka rika yi a gwamnatin Buhari ne ya gurgunta darajar Naira – Oshiomhole

Sanata Adams Oshiomhole, ya zargi tsohuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da taka raws wajen gurgunta tattalin arziki Nijeriya

Ya bayyana hakan a wani taro na kungiyar gwamnoni da aka gudanar a garin Benin, jihar Edo, a ranar Asabar, Oshiomhole din nan kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.

Inda ya ce yawaita buga sabbin takardun kudi na Naira da babban bankin kasar CBN ya rika yi a lokacin gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari ya taka muhimmiyar rawa wajen gurgunta Nijeriya

Oshiomhole ya ce suna da kundin bayanai da suka tabbatar da cewa an buga sabbin takardun kudi sama da tiriliyan 31 a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata