Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiYawan man fetur din da ake sha a Nijeriya ya ragu da...

Yawan man fetur din da ake sha a Nijeriya ya ragu da kaso 16 cikin 100 – NMDPRA

Hukumar NMDPRA ta bayyana cewa yawan amfani da man fetur a Najeriya ya ragu da kashi 16.42 cikin dari a watan Yunin 2025 zuwa lita biliyan 1.44, daga lita biliyan 1.77 da aka shaida a watan Mayu.

Daraktan hulda da jama’a na hukumar, George Ene-Ita, ya ce matsakaicin adadi na yawan bukatunsa a kullum ya tsaya a lita miliyan 48.02.

An kuma samu karin kashi 1.73 cikin 100 wajen samar da dizal zuwa lita miliyan 432.18, amma rarrabawar ta ragu da kashi 23.23 zuwa lita miliyan 424.06.

Samar da kananzir ya ragu da kashi 13 cikin 100 zuwa lita miliyan 7.79, yayin da samar da man mota ya fadi da kusan kashi 48 cikin 100 zuwa sama da lita miliyan 37 a fadin Nijeriya kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata