Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaYawan tarin jam'iyyu na lalata gwamnati, in ji Ganduje

Yawan tarin jam’iyyu na lalata gwamnati, in ji Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu laifi a yi tsarin jam’iyya daya idan har hakan ne ‘yan Nijeriya ke so.

Ganduje ya bayyana hakan ne bayan jagorantar Sanatoci uku na jam’iyyar PDP daga jihar Kebbi zuwa wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Juma’a gabanin sauya shekar su zuwa jam’iyyar APC.

A cewar Ganduje, jam’iyyun siyasa da yawa suna lalata gwamnati.

Ya ce mafi yawan ‘yan jam’iyyun da suke dawowa jam’iyyar APC na komawa jam’iyyar saboda sunga kyakkyawan tsarin shugabanci da ke gudana a APC.

A cewarsa, kasar Sin tana daya daga cikin kasashe masu karfin fada aji a duniya, kuma tsarin jam’iyya daya ce suke amfani da shi dan haka ba abin kunya bane dan an yi tsarin jam’iyya daya a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata