Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiYunwar mulki ce ke damun Atiku, El'rufai da Obi - Jam'iyyar APC

Yunwar mulki ce ke damun Atiku, El’rufai da Obi – Jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta soki kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da kuma tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da suka yi cewa shugaba Bola Tinubu na amfani da talauci a matsayin makamin wajen hana ‘yan Nijeriya su juya masa baya.

Jiga-jigan siyasar uku sun yi wannan ikirarin ne a karshen mako wajen taron da aka gudanar a Abuja don murnar cika shekaru 60 na Rotimi Amaechi.

A wata sanarwa da ya fitar, kakakin jam’iyyar APC, Felix Morka, ya caccaki ‘yan siyasar uku, inda ya ce sun kasa kawar da talauci a jihohinsu ko kasar duk da cewa sun rike kujerun gwamnati a lokaci daban-daban

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata