Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiZa a rufe sansanin 'yan gudun hijra na Muna da ya shafe...

Za a rufe sansanin ‘yan gudun hijra na Muna da ya shafe shekaru 10 a jihar Borno

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum Umara ya ce, nan da mako daya za a rufe sansanin ‘yan gudun hijira na Muna da ke dauke da ‘yan gudun hijira sama da 11,000.

Sansanin na Muna na daya daga cikin manyan sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar wanda aka samar shekaru 10 da suka gabata.

Gwamna Zulum ya bayyana rufe sansanin ne a lokacin da ya kai ziyara a sansanin a makon da ya gabata, inda ya bayyana munanan dabi’un da ake aikatawa a matsayin babban dalilin rufe sansanin.

Ya kuma kara da cewa, dole ne ‘yan gudun hijirar su koma gidajensu domin neman na kansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata