Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiZa a yi binciken kwakwaf a kamfanin NNPCL nan ba da jimawa...

Za a yi binciken kwakwaf a kamfanin NNPCL nan ba da jimawa ba – Gwamnatin Nijeriya

Ministan kudin Nijeriya ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a fara binciken kwakwaf a kamfanin man fetur na kasa NNPCL.

Da yake jawabi a wurin taron masu saka hannun jari na Najeriya da ke gudana a gefen taron asusun bada lamuni na duniya IMF da Bankin Duniya a birnin Washington na Amurka, Edun ya bayyana cewa sauyin shugabancin kamfanin NNPC na daga cikin matakan tsaftace kamfanin da gwamnatin tarayya ta dauka.

Ministan ya bayyana muhimman sauye-sauye da gwamnatin tarayya ta aiwatar don sake farfado da tattalin arzikin kasar da kuma sanya kwarin gwiwa ga masu zuwa hannun jari.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata