Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaZa mu karɓi Kwankwaso idan ya yanke shawarar koma wa APC- Ganduje

Za mu karɓi Kwankwaso idan ya yanke shawarar koma wa APC- Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta karɓi tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, idan har ya yanke shawarar dawowa jam’iyyar.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da Ministan Jiha na Ma’aikatar Gidaje da Cigaban Birane, Hon. Yusuf Ibrahim Atah, ya kai masa ziyarar ban girma a hedikwatar APC da ke Abuja.

Ya ce, idan mutum yana neman mafaka daga gida guda, wajibi ne a buɗe masa ƙofa, musamman idan akwai dangantaka ta siyasa da tarihi tsakaninsu.

A baya -bayan nan rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar APC na ci gaba da karɓar sabbin mambobi daga sauran jam’iyyu, musamman a wasu jahohin da ke fama da rikicin siyasa na cikin gida.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata