Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiZa mu kara shiga yajin aiki muddin aka sake dakatar da ma’aikatanmu...

Za mu kara shiga yajin aiki muddin aka sake dakatar da ma’aikatanmu – PENGASSAN

Kungiyar manyan ma’aikatan mai da iskar gas PENGASSAN, ta kalubalanci fadar shugaban Nijeriya bisa kalaman mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima kan rikicinsu da matatar man Dangote.

PENGASSAN ta shaida wa jaridar Punch a ranar Litinin cewa, za ta cigaba da daukar matakin shiga yajin aiki matukar aka sake korar mambobinta.

Martanin ya biyo bayan da wasu al’umma a jihar Kaduna da suka gudanar da zanga-zanga inda suke zargin PENGASSAN da yi wa matatar Dangote zagon-kasa.

A ranar Litinin ne mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya gargadi kungiyar PENGASSAN da cewa, Nijeriya tana gaba da kowa kuma Dangote na daga cikin kashin bayan ci-gaban tattalin arzikin Nijeriya.

Sai dai, a martanin da shugaban kungiyar, Festus Osifo ya yi wa Shettima ya ce Nijeriya tana gaba da Dangote da kuma fadar shugaban kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata