Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaZa mu tabbatar da Shugaba Tinubu ya yi tazarce a zaben 2027...

Za mu tabbatar da Shugaba Tinubu ya yi tazarce a zaben 2027 – Yahaya Bello

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana goyon bayansa ga sake zaben shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

A wata sanarwa da daraktan ofishin yada labaransa, Ohiare Michael, ya fitar, Bello ya ce Tinubu da tawagarsa sun yi kokari matuka duk da kalubalen duniya ke fuskanta na matsin tattalin arziki.

Bello ya karyata rade-radin cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, yana zargin wasu da kokarin haddasa rikici tsakaninsa da shugaba Tinubu.

Ofishinsa ya gargadi jama’a da kada su yarda da labaran karya da marasa aikin yi ke yadawa a kafafen sada zumunta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata