Kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi wa Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, na yin murabus ko kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi daga muƙaminsa.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a martani ga kalaman Sakataren Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ya buƙaci Wike ya ajiye aikinsa na minista domin ya mayar da hankali kan rikicin siyasar jihar Rivers.
DCL Hausa ta ruwaito cewa wannan cece-kuce na zuwa ne bayan gargaɗin da Wike ya yi wa Ajibola Basiru kan tsoma baki a rikicin siyasar Rivers, inda ministan ke cikin takaddama da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara.
A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar, Saleh Zazzaga, ya fitar, kungiyar ta ce babu dalilin da zai sa a sauke Wike, tana mai jaddada cewa Birnin Tarayya Abuja na cikin yankin Arewa ta Tsakiya, kuma Wike yana aiwatar da aikinsa yadda ya dace.
