Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya isa Babbar Kotun Jihar Kaduna domin ci gaba da shari’arsa da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC.
Kotun ta dage sauraron bukatar belin da ya gabatar zuwa ranar 14 ga Afrilu.
Hukumar ICPC ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda 10, wadanda suka hada da zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma wawure kudade kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Ga wasu daga cikin hotunan Nasir El-Rufa’i a lokacin da ya isa kotu: Credit: Daily Trust

