DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnonin Arewa sun nemi ‘yan majalisa da su yi watsi da kudirin sake fasalin haraji da Tinubu zai yi

-

Gwamnan Bauchi/Gwamnan Jigawa/Gwamnan Gombe

Wani sabon rikici ya kunno kai game da batun sake fasalin haraji a gaban Majalisar Dokoki ta Kasa, yayin da gwamnonin Arewa suka fito fili suka yi watsi da wasu shawarwarin, musamman tsarin raba harajin VAT a daya daga cikin kudirorin.

Gwamnonin Arewa dai sun cimma wannan matsaya ne a ranar Litinin bayan wani taro da suka yi a Kaduna dake arewa maso yammacin Nijeriya.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Uba Sani na jihar Kaduna, Inuwa Yahaya na Gombe, Dauda Lawal Dare na Zamfara, Abdullahi Sule na Nasarawa, Babagana Zulum na Borno, Bala Mohammed na Bauchi, AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, da Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa.

Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya a lokacin da yake karanta sanarwar daga taron, ya ce kudaden harajin ya saba wa muradun Arewa, ya kuma umurci ‘yan majalisar Arewa da su yi watsi da kudirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar...

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Mafi Shahara