DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An sake fasalta masu magana da yawun Shugaba Tinubu

-

 

Google search engine

Sunday Dare, Daniel Bwala da Bayo Onanuga su ne masu magana da yawun shugaban kasa – fadar gwamnatin Nijeriya. 

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya sake nada mukamai guda biyu na mutanen da za su rika magana da yawun fadar shugaban kasa. 

Wata sanarwa da Hadimin shugaban ƙasa kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce yanzu ba mutum daya ne zai riƙa magana da yawun shugaban ba. 

Ko baya ga shi Bayo Onanuga, shugaba Tinubu ya amince da naɗa Mista Sunday Dare da kuma Daniel Bwala a matsayin masu ba shi shawara akan yada labarai da harkokin sadarwa. 

Wannan dai wani mataki ne da ake kallo garambawul da gwamnatin ke yi, a cewar jaridar Premium Times.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An fitar da jihohi 4 a Gasar Kokawar Nijar ta 2025

Kwana na uku da fara gasar kokawar gargajiya a Nijar tuni an yi waje da jihohi hudu daga cikin takwas na kasar daga jerin wanda...

Ya kamata a canza salon yadda ake yakar ‘yan bindiga a Nijeriya

Daga: Farfesa Usman Yusuf Litinin : 22 Disamba 2025 Ban taɓa gudu ko ja da baya ba ko nuna wata fargaba wajen bayyana matsayina a kan yaƙin...

Mafi Shahara