DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tarin bashin da kake ciyowa ke jikkata tattalin arzikin Nijeriya, sakon Atiku Abubakar ga Shugaba Tinubu

-

Google search engine

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, ya ce tarin bashin da gwamnatin APC ke ciyowa na kassara tattalin arzikin kasar.

Atiku ya kuma zargi majalisar dokoki ta kasar da zama taimakawa wajen jefa kasar cikin bashi.

Da yake martani kan bashin da majalisar ta amince Tinubu ya ciyo na baya-bayannan, Atiku ya ambato wani rahoto na bankin duniya wanda ya ce ya dora Nijeriya a mataki na uku cikin kasashen da tulin bashi ya yi wa yawa.

Tsohon shugaban ya bayyana damuwa aka yadda gwamnatin ke ci gaba da cin bashi, duk da cewa a watan Yuli shugaba Tinubu ya ce hukumar tattara haraji ta kasa da hukumar kwastam sun samar da kudade ga kasar wadanda ba a taba gani ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Nijeriya za ta kara mayar da hankali kan tsaurara matakan kudi da gyaran haraji a 2026 – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa shekarar 2026 ta zo da sabon mataki mai karfi na bunkasar tattalin arziki, inda ya ce gyare-gyaren...

Bankunan Nijeriya za su fara cire harajin N50 daga masu tura kudi ta banki da suka kai N10,000

Daga 1 ga watan Janairun, 2026, bankunan Nijeriya za su fara cire harajin N50 kan duk wanda ya tura kudi da ya kai ₦10,000 ko...

Mafi Shahara