DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan Katsina ya nada sabon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar

-

Gwamnan jihar Katsina ya amince da nadin Hon Abdulƙadir Mamman Nasir a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.
Abdulƙadir Mamman Nasir ya maye gurbin Hon Jabiru Abdullahi Tsauri wanda Shugaba Tinubu ya nada mukami a Abuja.
Kafin nadin na Hon Abdulƙadir, shi ne shugaban hukumar kula da nomar rani ta jihar Katsina wato Katsina Irrigation Authority.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Gwamnan Malam Ibrahim Kaulah Mohammed da DCL Hausa ta samu kwafi a Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Cin hanci la’ana ce, mu tsabtace kanmu daga rashawa- EFCC

A wani sakon tunatarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook albarkacin ranar Juma’a, hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya,...

Babu karar-kwana, da tuni na bakuncin lahira a zanga-zangar #EndSARS – Jarumi a Nollywoood Desmond Elliot

Fitaccen ɗan wasan fina-finan Nollywood kuma ɗan siyasa, Hon. Desmond Elliot, ya bayyana yadda ya kuɓuta daga wani hari da wasu baƙin fuska suka yi...

Mafi Shahara