DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar shirya Gasar Firimiyar kwallon kafa ta Najeriya ta bada hutun wasanni

-

Hukumar shirya gasar kwallon kafa ta Firimiyar Najeriya NPFL, ta ayyana hutun tsakiyar gasar bana ta 2024/25, na wasannin zagayen farko.
A cikin sanarwar da hukumar ta rabawa manema labarai, hukumar ta ce za a dawo hutun ne domin ci gaba da zagaye na biyu na gasar a ranar 25 ga Janairun 2025, bayan shafe makonni uku ana hutu.
Haka zalika hukumar ta bayar da damar bude cinikayyar ‘yan wasa wato ‘Transfer’ daga Ranar 6 ga Janairu zuwa Fabrairu 5 ga watan 2005. 
Kungiyar Remo Stars ce ke jagorancin teburin gasar da maki 36, yayin da Rivers United ke rufa mata baya da maki 34.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar...

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Mafi Shahara