DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu a Amurka ta umurci FBI da hukumar yaki da muggan kwayoyi da ta saki bayanan bincike kan Shugaba Tinubu

-

Bola Ahmad Timubu

 Wata kotu a Amurka ta umurci manyan jami’an tsaron kasar da su fitar da bayanan sirri da aka samu kan Shugaba Bola Tinubu a lokacin wani binciken da gwamnatin ta yi a shekarun 1990.

Alkalin kotun, Beryl Howell, ya ba da umarnin ne, yana mai cewa rufe bayanan ba’a bayyana wa jama’a ba, ba abu ne mai ma’ana ba.

Ba’amurke, Aaron Greenspan ne, ya shigar da kara a watan Yunin 2023 a karkashin dokar ‘yancin fitar da bayanai (FOIA) ofishin zartarwa na lauyoyin Amurka, ma’aikatar bincike ta (FBI),hukumar kula da magunguna (DEA), da hukumar leken asiri ta (CIA).

A cikin korafin nasa, Greenspan ya zargi hukumomin tsaro da karya dokar FOIA ta hanyar gaza fitar da bayanan cikin lokacin da aka kayyade, takardun da suka shafi binciken kan Shugaba Tinubu da wani Abiodun Agbele.

  1. Agskiya bola tunubu bamutumin kirki bane saboda baya tausayawa masu rauni daga cikin bayun Allah Wanda yakeci da haqqinsu.
    Muna rokon Allah ya kwacemu daga hannu wannan Azzalumi.
    Ameen

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta karɓi wasikun kulla kawance daga sabbin jakadun ƙasashe 8

A ranar Juma’a, 9 ga Mayu, 2025, fadar gwamatin ta Jamhuriyar Nijar ta karɓi sabbin jakadun daga jakadun ƙasashen duniya guda takwas. Inda shugaban mulkin sojin...

Cin hanci la’ana ce, mu tsabtace kanmu daga rashawa- EFCC

A wani sakon tunatarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook albarkacin ranar Juma’a, hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya,...

Mafi Shahara