DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu masoyi ne ba makiyin arewa ba – Minista Bello Matawalle

-

Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya Bello Matawalle, ya yi watsi da ikirarin da masu sukar gwamnati ke yi cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba mai son ci gaban yankin Arewacin Nijeriya ne ba, yana mai cewa Shugaban kasar ya jajirce wajen magance dimbin kalubalen da yankin ke fuskanta.

A wata sanarwa da babban mataimakin ministan kan harkokin siyasa Ibrahim Danmaliki Gidan Goga ya fitar, Matawalle ya bayyana cewa dimokuradiyya ta samu gindin zama a Nijeriya karkashin Shugaba Tinubu fiye da kowane lokaci.

Google search engine

Ya ce masu yi masa kalaman na cewa Tinubu ba masoyin arewa ne ba, na amfani da farfaganda da karya ne don neman cimma muradunsu na siyasa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

PDP ta dage tantance ‘yan takara na babban taronta na kasa

Dagewar ta zo ne ’yan sa’o’i bayan tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ayyana shirinsa na takarar shugabancin jam’iyyar, duk da cewa wasu...

Ina matukar tausayin mazaje masu mata daya, in ji Sanata Ned Nwoko

Ina matukar tausayin mazaje masu mata daya, akwai nutsuwa tattare da auren mace fiye da daya, in ji wani Sanata daga kudancin Nijeriya Sanata Ned Nwoko...

Mafi Shahara