DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jam’iyyar PDP a shirye take domin tunkarar zaben 2027 – Samuel Anyanwu

-

Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Samuel Anyanwu, ya bayyana jin dadinsa da irin shirye-shiryen da jam’iyyar ke yi gabanin zabukan 2027 a jihar Imo da Nijeriya.

Anyanwu, ya bayyana hakan ne a karshen mako, lokacin da yake jawabi ga kwamitin zartarwar jam’iyyar PDP a jihar Imo, wanda ya hada da shugabanni da masu ruwa da tsaki a sakatariyar jam’iyyar a Owerri, jihar Imo.

Google search engine

Ya ce dole ne ‘ya’yan jam’iyyar su yi aiki kafada da kafada domin cimma burinsu na kwace mulki hannun APC, yana mai cewa zaben gwamna na da muhimmanci ga jam’iyyar domin karbar mulki a jihar Imo.

Anyanwu ya ce mutanen Imo sun gaji da yaudara da gwamnatin yanzu ke yi don haka akwai bukatar a tsaya kai da fata domin yin nasara a zabuka masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Matsayin da nake da shi a kungiyar dattawan Yammacin Afrika ya sa na janye daga harkokin siyasa – Jonathan

Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa zama memba a Dandalin Dattawan Afrika ta Yamma (WAEF) shi ne babban dalilin da ya hana shi...

‘Yan bindiga sun kuma sace dalibai a jihar Neja

Rahotannin da jaridar Daily Trust ta samu sun ce barayin daji sun yi garkuwa da dalibai da ma’aikatan da har ya zuwa ynzu ba a...

Mafi Shahara