DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar NAHCON ta saka ranar da maniyyata aikin hajjin Nijeriya na 2025 za su fara tashi zuwa Saudiyya

-

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON a cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yada labaran hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar, ta tunatar da shugabannin hukumomin jin dadin alhazai na jihohi cewa hukumar na yin shiri na karshe kafin a fara jigilar mahajjata daga ranar ranar 22 ga watan Afrilu 2025.

Shugaban hukumar Farfesa Abdullah Saleh Usman wanda ya gana sakatarorin hukumomin, ya yi kira ga shugabannin da su ci gaba da wayar da kan alhazai wajen yin rigakafi tare da tabbatar da yin duk wasu abubuwa da ake bukata.

Google search engine

A yayin taron an bayyana cewa jirgin Air Peace zai dauki alhazai 5,128 daga jihohin Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Ondo, Rivers, Taraba da Taraba.

Sai kuma kamfanin FlyNas an ware masa maniyyata 12,506 daga Abuja, Kebbi, Lagos, Ogun, Osun, Sokoto da Zamfara, yayin da kamfanin Max Air zai yi jigilar alhazai daga jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kwara, Oyo da Plateau.

Kamfanin Umza kuwa zai yi jigilar maniyyata 10,163 daga jihohin Kaduna, Adamawa, Nasarawa, Neja da Yobe.

Sanarwar ta ce kusan alhazai 43,000 ne za su sauka a kasa mai tsarki domin yin ibadar aikin hajjin shekarar 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

El-Rufai ya nemi Ribadu ya yi karin haske kan ‘gubar’ thallium sulphate mai matukar hatsari

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bukaci Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, da ya fayyace rahotannin...

Hadin kan siyasa na karuwa a Kano – Gwaman Kano

Gwamnan Kano State, Abba Kabir Yusuf, ya ce ana samun ci gaba a hadin kan siyasa a jihar, yana mai fatan rikicin masarautar Kano zai...

Mafi Shahara